Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kokarin samarwa masu zuba jari na gida da na waje yanayin kasuwanci bisa ka'idoji iri daya
2019-10-24 11:52:29        cri

A jiya Laraba, gwamnatin kasar Sin ta fitar da dokar ka'idojin kyautata yanayin kasuwanci. A cikin wannan dokar, an fitar da wasu sabbin ka'idoji, ta yadda take son kawar da wasu matsaloli wadanda masu zuba jari na gida da na waje suke fuskanta, da kuma yin kokarin kyautata yanayin kasuwanci bisa doka.

Wannan doka na kunshe da babi 7 tare kuma da tanade-tanade 72, wadanda suke shafar bangarori daban daban game da yadda za a kyautata yanayin kasuwanci bisa doka. A wani taron manema labaru da ofishin yada bayanai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a jiya Laraba, Mr. Ning Jizhe, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin bunkasa da yin gyare-gyare na kasar Sin yana mai bayyana cewa,"Bisa sabon tunanin neman bunkasuwa, da daidaita alakar dake tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa yadda ya kamata, da kuma kyautata tsarin tattalin arziki bisa ra'ayin gurguzu da dai makamantansu, an zana da kuma kafa wasu muhimman ka'idoji a cikin dokar, sannan an yi nazari kan wasu muhimman matsalolin da ake fuskanta, alal misali, ta wadanne hanyoyi ne za'a iya kare wadanda suke neman bunkasa kasuwanci? Yaya za a iya tsabtace yanayin kasuwa? Da kuma yaya za a sa ido kan kasuwanci bisa bin doka da dai sauransu, an fitar da wasu matakan warware su baki daya, ta yadda za a iya sanya gwamnatocin matakai daban daban da su yi gyare-gyare kan ayyukan da suke yi."

A 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta dauki dimbin matakai ta yi kokarin yin gyare-gyare wajen kara kyautata yanayin kasuwanci. Yanzu, a bayyane ne yanayin kasuwanci da kasar Sin take ciki ya samu kyautatuwa sosai. Amma babu wata dokar dake iya tabbatar da ganin an aiwatar da wadannan matakai kamar yadda ya kamata. Mr. Zhang Yaobo, wanda ke kula da aikin kafa dokoki a ma'aikatar shari'ar kasar Sin ya bayyana cewa, "An mayar da wasu matakan kyautata yanayin kasuwanci da sa ido kan kasuwa da dai makamantansu da aka dauka a 'yan shekarun baya don su zama tanade-tanade a cikin wannan doka. Sakamakon haka, wadannan matakai za su iya zama abubuwan tilas da dole ne kowa ya bi. Wannan doka za ta iya kara tabbatar da tsayawa kan kokarin kyautata yanayin kasuwanci."

A ganin Ning Jizhe, a cikin kyakyawan yanayin kasuwanci, za a iya kara bude kofar kasar Sin ga ketare domin hanzarta harkokin yin gyare-gyare da kuma kara neman bunkasuwa, sannan kafa wani yanayin kasuwanci, inda ake da adalci, amma babu nuna bambanci ga dukkan kamfanoni, ciki har da kamfanoni masu jarin waje. A cikin wannan doka, an mayar da manufofin kafa wani sabon tsarin tattalin arziki dake bude kofarsa ga ketare baki daya su zama ka'idojin doka, kuma an yi amfani da kalmomin doka wajen tabbatar da manufar kasar Sin ta kara bude kofarta ga ketare. Sakamakon haka, za a iya samar da tabbaci bisa doka ga duk wanda yake son shigar da jarin waje a kasar Sin, da kuma bunkasa tattalin arzikin zamani mai inganci. Ning Jizhe yana mai cewa, "Da farko dai, an tabbatar da cewa, ya kamata a kyautata yanayin kasuwanci bisa bukatar da ake da ita a kasuwa bisa doka, da wasu ka'idojin da ake bi a duk fadin duniya. Sannan za a kula da dukkan kamfanonin gida da na waje bisa doka iri daya, da ka'idoji iri daya. Bugu da kari, ana fatan dokar za ta taka rawar a zo a gani wajen shigar da jarin waje a kasar Sin. Na biyu, an tabbatar da cewa, za a kafa wani tsarin kasuwanci dake bude kofa ga ketare, kuma za a iya yin takara cikin adalci. Bugu da kari, za a iya cinikin dukkan kayayyakin da ake bukata wajen samar da kayayyaki a kasuwa ba tare da shinge ba. Na uku shi ne, a bayyane ne an nemi duk wanda yake son yin cinikin waje ya bi ka'idojin da ake bi a galibin yankunan duniya."

Daga karshe dai, Mr. Ning Jizhe ya ce, kasar Sin na maraba da kamfanoni masu jarin waje da su kara zuba jari a kasar Sin da kuma yin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin, ta yadda za su iya samun moriya da nasara tare. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China