Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gaggauta kyautata cinikin waje
2019-10-24 10:56:34        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta gaggauta daukar wasu matakai na yin sauye sauye domin daga matsayin cinikin wajenta, ministan kasuwancin kasar Zhong Shan ya tabbatar da hakan.

Zhong ya bayyana karuwar cinikin wajen kasar a matsayin mai karuwa cikin sauri a lokacin da yake gabatar da rahoton aiki ga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin jiya.

Adadin cinikin wajen kasar Sin ya kai kaso 11.8% dake cikin daukacin adadin cinikin wajen kasashen duniya a shekarar 2018, amma a shekarar 1950 ya kai kaso 1% kawai, wato ya tsallaka zuwa matakin farko a duniya daga matsayi na 28.

Zhong ya ce, gwamnatin kasar za ta dauki matakan kara kyautata tsarin cinikin wajenta a nan gaba, inda za ta mayar da hankali wajen yin hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Haka zalika, kasar Sin za ta daga matsayin gina yankunan cinikayya ta intanet na gwaji, da kuma zurfafa yin gyare gyare da kara bude kofa a bangaren cinikin samar da hidima.

Domin cimma nasarar daidaita yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya ba tare da bata lokaci ba, Zhong ya ce, kasar Sin za ta ingiza matsayin kafa cibiyoyin kasuwanci marasa shinge na gwaji.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China