Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi zaben yan majalisu a Botswana
2019-10-24 09:59:04        cri

An gudanar da zaben 'yan majalisu a kasar Botswana a jiya Laraba, inda jama'ar kasar suka jefa kuri'a don zabar 'yan majalisar dokoki na kasa 57 gami da na jihohi 490.

Yayin da yake hira da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, kakakin kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Botswana, Osupile Maroba, ya ce an gudanar da zaben a wurare daban daban na kasar lami lafiya, karkashin sa idon da tawagogin kungiyar tarayyar Afirka AU da kungiyar raya kudancin Afirka SADC suka yi.

Zaben na wannan karo shi ne irinsa na 12 da ya gudana tun bayan da Botswana ta samu 'yancin kai a shekarar 1966. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China