Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malamin da ya yi zane da rairayi
2019-10-25 10:58:40        cri

 

 

 

 

 

Malam Alateng Bilige ke nan mai shekaru 37 a duniya, wanda ke rayuwa a gundumar Zhenglan da ke jihar Mongoliya ta kasar Sin. Ya shawara wajen yin zane da rairayi. Kasancewar gundumar Zhenglan cikin hamadar Hunshandak, ana iya samun rairayi masu launukan baki da fari da ja da rawaye a wurin, don haka, malamin ya kan debo rairayin daga hamadar ya tace ya kuma wanke shi, sa'an nan ya yi zane da shi. Zanen da ya yi na samun karbuwa sosai, kuma yana samun yuan sama da miliyan a kowace shekara daga zanen da ya yi kuma ya sayar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China