Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya musanta zargin da aka yi mata kan hakkin Bil Adama
2019-10-23 10:44:36        cri

Game da zargi maras tushe da wasu kasashe ciki hadda Amurka suka yiwa kasar Sin kan harkokin Xinjiang da Hong Kong, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya ba da jawabi a zaman kwamiti na uku na babban zauren MDD karo na 74 da aka yi a jiya Talata, inda ya musanta zargin maras tushe da aka yi, wanda ya ce fakewa ne da batun kare hakkin Bil Adama don tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, da kuma ingiza fito-na-fito ga kasar Sin cikin MDD.

Zhang Jun ya bayyana a gun taron da aka yi na kwamiti na uku cewa, wasu kasashe ciki hadda Amurka suna ci gaba da yunkurin fakewa da batun hakkin Bil Adama don yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, inda ya ce Sin na nuna matukar rashin jin dadi da adawa da hakan.

A cewarsa, ba za a hana bunkasuwar duniya ba, kuma ba wanda zai iya cin zarafin wani bisa karfinsa. Amma, wasu kasashe na yunkurin shiga gonar sauran kasashe da ba da umurni yadda suke so. Ya ce kasar Sin na kira ga wadannan kasashe da su yi watsi da manufar babakere da kama karya, wadanda kuskure ne da ba su dace da halin da ake ciki a yanzu ba.

Zhang Jun ya kara da cewa, laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani. Yana mai cewa wasu kasashe na tada zaune tsaye a wurare daban-daban da kuma yunkurin hambarar da gwamnatocin sauran kasashe, matakan da ya keta hakkokin Bil Adama a sauran kasashe, sannan ba sa tunanin hali maras kyau da suke ciki ko kadan a wannan fanni. Ya kara da cewa, suna kira da wadannan kasashe da su san laifinsu da kuma gudanar da harkokinsu na cikin gida yadda ya kamata, sannan su kaucewa rura wuta a sauran wurarwe. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China