Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban hada-hadar cinikayya ta yanar gizo na ciyar da tattalin arzikin kasar Sin gaba
2019-10-22 20:21:11        cri

 

A yanayin da ra'ayin kashin kai da ba da kariya ke ci gaba da tsananta, da ma yadda tattalin arzikin duniya ke kara fuskantar matsin lamba, tattalin arzikin kasar Sin na canja salo daga saurin bunkasa zuwa samun ci gaba mai inganci, a waje guda kuma yana fuskantar kalubale na raguwar kason da ya samu a duniya a fannin kayayyakin dake bukatar ma'aikata da ayyuka da yawa. Sai dai yawan al'ummar kasar Sin da makomar kasuwarta mai kyau sun samar da yanayi mai kyau ga bunkasa hada-hadar cinikayya ta yanar gizo, kuma hakan na iya kara karfin takarar kasar Sin a fannin tattalin arziki a fadin duniya.

A shekarar 2018, hada-hadar cinikayyar kasar ta yanar gizo ya kai kaso 34.8 bisa na GDPn kasar Sin, adadin da ya kai triliyan yuan 31.3. Ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin sana'o'in yanar gizo, zai ba da gudummawa ga bangaren tattara bayanai da na sadarwa, yayin da zamanintar da sashen zai ci gaba da taka rawa wajen yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin da daga matsayin sa, hada-hadar cinikayya ta yanar gizo kuma za ta samar da manyan guraban ayyukan yi ga kasar ta Sin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China