Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kan ba da taimako ga ketare bisa tushen daidaito da cin moriya tare da bude kofa da samar da taimako mai dorewa
2019-10-22 16:27:09        cri

Jiya Litinin, kwamiti na uku na babban zauren MDD karo na 74 ya gudanar da taron tattaunawa da masana masu nazarin basusuka.

Wakiliyar musamman mai kula da harkokin kare hakkin Bil Adama ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Liu Hua ta nuna cewa, Sin ta kan ba da taimako bisa ka'idoji masu tushe guda 4, na farko, nuna adalci, Sin ta kan ba da taimako bisa mutunta burin gwamnati da jama'ar sauran kasashe, ba ta taba tsoma baki cikin harkokin wata kasa ba, kuma ba tare da ko wani sharadi ba; na biyu kuma, Sin na ba da taimako don cin moriya tare, da la'akari da halin da kasa ke ciki a fannin tsarin kudi a dogon lokaci; na uku kuma, bude kofa ga kowa, Sin na kokarin kara hadin kai da sauran kasashe; na hudu kuwa, ba da taimako mai dorewa, da koyar da dabaru da fasahohi, ta yadda sauran kasashe za su samu bunkasuwa mai dorewa da dogaro da kansu.

Liu Hua ta ce, Sin na fatan hadin kai da bangarori daban-daban don ba da gudunmawarta wajen kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai bude kofa ga kowa, da samun daidaito da kuma samun wadata baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China