Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na da bayanai da tunani masu dimbin yawa
2019-10-22 14:30:04        cri

Jiya Litinin a gogon wurin, kwamiti na uku na babban zauren MDD karo na 74 ya gudanar da taron tattaunawa da ma'aikata na musamman masu ba da rahoto kan batun fadin albarkacin baki.

Wakiliyar musamman mai kula da harkokin kare hakkin Bil Adama na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Liu Hua ta nuna cewa, dokoki da tsarin shari'ar kasar Sin suna mutunta hakkin jama'arta na fadin albarkacin bakinsu. Gwamnatin kasar Sin kuma ta kafa dandalolin yanar gizo ta Intanet don baiwa jama'a damar fadin albarkacin bakinsu bisa doka.

Bayanai na cewa, a shekarar 2018, yawan mutane da suka shiga shafin Intanet ya kai miliyan 829, yawan bayanan da aka wallafa a ko wace rana ya kai fiye da biliyan 30. Yawan litattafai da aka wallafa a fannoni daban-daban ya kai biliyan 9.5 a ko wace shekara, yawan jaridu da mujalolin kasar ya kai nau'o'i dubu 12. Matakin da ya sa, Sin ta samar da bayanai mafiya yawa a duniya, kuma na da tunani masu dimbin yawa.

Liu Hua ta nuna cewa, ya kamata, kasashe daban-daban su yi musanyar ra'ayi kan yadda za a kafa tsarin daidaita Intanet bisa tushen mutunta juna, ta yadda za a tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki bisa doka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China