Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taka rawar gani wajen raya fasahar 5G
2019-10-22 11:12:06        cri


Kwanan baya an shirya dandalin tattaunawa kan fasahar sadarwar intanet ta tafi da gidanka na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Zurich na Switzerland, inda masanin fasahar sadarwa Ken Rehbehn dake aiki a shahararriyar kungiyar hasashen tattalin arziki da bada shawarwari kan harkokin kasuwanci HIS Markit ya bayyana cewa, yana gudanar da bincike mai zurfi kan ci gaban fasahar 5G da kuma rawar da kasar Sin take takawa a bangaren ingiza ci gaban fasahar.

Ken Rehbehn, wanda ya dade yana gudanar da aikin nazarin fasahar sadarwa ta tafi da gidanka, ya gaya mana cewa, ci gaban fasahar 5G yana dogaro ne kan goyon bayan manufofin kasa da kuma fasahohi masu inganci, yana mai cewa, "Idan ana son raya fasahar 5G, dole ne a samu goyon bayan daga wajen gwamnatin kasar, haka kuma ana bukatar goyon bayan kamfanoni masu samar da na'urorin da abin ya shafa kamar Huawei, ina ganin cewa, goyon bayan manufofin gwamnati da kamfanonin samar da na'urorin fasahar zamani sharadi ne da ya zama wajibi ga aikin raya fasahar 5G."

Ken Rehbehn ya dauka cewa, ya dace a kara saurin sadarwar intanet ta tafi da gidanka cikin gajeren lokaci ta hanyar yin amfani da fasahar 5G, kuma ya dace a kara habaka amfanin fasahar a sauran fannoni, yana mai cewa, "A cikin gajeren lokaci, fasahar 5G zata taka rawar gani wajen samar da karin bayanai ta yanar gizo, kamar yadda ake ganin yanayin da ake ciki a kan hanyar mota mai saurin tafiya, idan hanya bata da fadi, amma motoci sun yi yawa, sai dai za a gamu da matsalar cunkoso, yanzu haka idan muna iya yin amfani da fasahar 5G yadda ya kamata, to zamu samu karin bayanan da muke bukata, a don haka muna sa ran cewa, zamu yi kokari domin yin amfani da fasahar a bangarorin nishadi da kuma kasuwanci."

Bisa hasashen da aka yi cikin dogon lokaci, Ken Rehbehn ya bayyana cewa, fasahar 5G zata taimaka wajen tafiyar da harkokin sana'o'i, tare kuma da ingiza ci gaban fasahar AI wato fasahar kwaikwayon tunanin bil Adama, a cewarsa: "Bisa shirin da aka tsara cikin dogon lokaci, zamu kara kyautata fasahar 5G bisa matakai daban daban domin kara saurinta, ta yadda za a tabbatar da cewa, za a iya sarrafa fasahar kamar yadda ake so, ina ganin cewa, a cikin shekaru 2 masu zuwa, zamu samu sakamako a bayyane."

Makasudin da kamfanin sadarwar Huawei na kasar Sin ya shirya dandalin tattaunawa kan fasahar sadarwar intanet ta tafi da gidanka na kasa da kasa na bana shine domin tattarawa da kuma more fasahohi da shawarwarin da shahararrun masanan da abin ya shafa da suka zo daga kasashe daban daban, domin ingiza ci gaban fasahohin zamani, inda Ken Rehbehn ya yi nuni da cewa, shirya dandalin muhimmiyar hanya ce da kasashen duniya suke gudanar da cudanyar dake tsakaninsu yayin da ake kokarin raya fasahar sadarwa, a cewarsa: "Har kullum muna jin dadin sauraren sakamakon fasahohin sadarwa da masanan kasa da kasa suka fada mana yayin dandalin, haka kuma muna jin mamaki matuka saboda babban ci gaban da aka samu a bangaren, kana an kuma bullo da matsaloli da kalubale da ake fuskantar a halin da ake ciki yanzu."

Ban da haka, Ken Rehbehn shi ma ya bayyana cewa, a bayyane ake lura cewa, kasar Sin tana taka babbar rawa wajen ci gaban fasahar 5G, yana mai cewa, "Da gaske ne kasar Sin tana taka rawar gani wajen ci gaban fasahar 5G, saboda gwamnatin kasar Sin ta riga ta bada fifiko kan aikin raya fasahar, lamarin da ya ingiza ci gaban fasahar cikin sauri, a sanadin haka, farashin wayar salula ya ragu, duk wadannan suna bayyana karin kirkire-kirkiren fasaha a kasar Sin, shi yasa ana iya cewa, idan gwamnatin kasar Sin bata samar da goyon baya cikin lokaci ba, to ba zai yiwu a samu ci gaban fasahar cikin sauri ba."

A sa'i daya, kasar Sin tana sanya kokari matuka domin tsara ma'aunin sadarwa iri guda na kasa da kasa domin sa kaimi kan ci gaban fasahar 5G a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China