Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Birtaniya ta wallafa kudurin dokar yarjejeniyar ficewar kasar daga EU
2019-10-22 10:56:50        cri
Gwamnatin Birtaniya ta wallafa kudurin dokar yarjejeniyar ficewar kasar daga Tarayyar Turai jiya da daddare, gabanin muhimmiyar muhawarar majalisar dokokin kasar a yau Talata.

Kudurin yarjejeniyar ya kunshi shafuka 110, tare da wasu shafuka 124 dake kunshe da bayanai.

Ana ganin matakin a matsayin wani yunkuri na gwamnatin kasar, na gaggauta zartas da dokar ta hannun majalisar da kuma amincewa da yarjejeniyar da Firaminista Boris Johnson ya cimma cikin kwanaki 3 kacal.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin ne ke shirya duk wasu harkokin da suka shafi gwamnati a majalisar.

A makon da ya gabata ne Birtaniya da Tarayyar Turai suka cimma yarjejeniyar ficewar Birtaniyar, amma yarjejeniyar na bukatar amincewar majalisar dokoki domin ta samu karfin doka kafin kuma Birtaniya ta samu damar ficewa daga Tarayyar.

Wallafa kudurin na zuwa ne sa'o'i bayan kakakin majalisar dokokin kasar John Bercow, ya ki amincewa da bukatar gwamnati na kada kuri'a kan yarjejeniyar da Birtaniya da EU suka cimma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China