Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Botswana ya yaba rawar da kamfanonin kasar Sin suka taka ga tattalin arzikin kasarsa
2019-10-21 11:38:38        cri
Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, ya ayyana sunayen wasu muhimman ayyukan more rayuwa uku wadanda kamfanonin kasar Sin daban daban suka gudanar a garin Francistown, birni mafi girma na biyu a kasar Botswana, kana ya yaba musu bisa rawar da suka taka wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Muhimman ayyukan uku sun hada da canza fasalin wata babbar hanyar mota wacce ake kira da spaghetti road, da gina filin wasa na Francistown, da kuma filin jirgin saman kasa da kasa na Francistown.

Masisi ya ce, aikin inganta titunan mota suna daga cikin muhimman abubuwan dake samar da bunkasuwar tattalin arzikin kowace kasa a duniya ciki har da kasar Botswana. Ya ce tilas ne ya yabawa kamfanonin gine-gine na kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da suka taka a harkokin ci gaban tattalin arzikin kasar Botswana.

Shugaban ya ce aikin gina hanyar motar zai taimaka matuka wajen saukaka zirga-zirgar jama'a da kayayyaki daga yankunan karkara zuwa biranen kasar.

Masisi ya ce muddin kasar tana son yin gogayya da sauran kasashen duniya ya zama wajibi a samu ingantattun hanyoyin mota da filayen jiragen sama makamantan wadanda kamfanonin kasar Sin suka gina. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China