Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen yammacin duniya na girbin abin da suka shuka sakamakon ma'auni iri biyu da suka dauka
2019-10-20 17:14:45        cri

 

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce a yankin Catalonia na kasar Spaniya, an kwaikwayi ayyukan keta dokoki na nuna karfin tuwo irin wanda ya faru a yankin Hong Kong na kasar Sin. Game da haka, gwamnatocin kasashen Burtaniya da Amurka wadanda ke goyon bayan ayyukan nuna karfin tuwo da aka tayar a Hong Kong sun yi shiru, wadancan kafofin watsa labaru na yammacin duniya dake kokarin karfafawa masu tayar da tashe-tashen hankula a Hong Kong gwiwa su ma sun canja ra'ayinsu kan irin lamari, sun yi zargi kan masu tayar da tashin hankali a yankin Catalonia, tare kuma da yin kira ga mahukuntan Spaniya da su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba.

Irin lamarin da ya faru a yankin Hong Kong, shi ne "aikin demokuradiyya", amma yanzu ya faru a Sapaniya, sai ya kasance "tashin hankali". Ma'auni iri biyu da kasashen yamma suka dauka kan lamari iri daya, ya nuna cewa, ra'ayin "'yancin kai da demokuradiyya" da suke bi, tamkar wasa ne bisa la'akari da moriyarsu, idan yana da amfani, sai su yi amfani da shi, idan ba ya da amfani, sai su yi watsi da shi, yanzu dai sun cire hijabin munafuncinsu na kutsa kai cikin harkokin yankin Hong Kong. Yanzu haka, kasashen yamma na girbar abin da suka shuka sakamakon shaguben da suka yi kan ayyukan nuna karfin tuwo da aka tayar a Hong Kong, lallai wannan shi ne "kaikayi koma kan mashekiya". (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China