Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru: Gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7 zata bunkasa cudanya da fahimtar juna
2019-10-20 16:45:18        cri
Gasar wasannin motsa jiki ta sojoji ta kasa da kasa karo na 7 wadda ake gudanarwa a kasar Sin ta samar da wani muhimmin dandali na kyautata cudanya da sada zumunci a tsakanin jami'an sojojin kasashe daban daban na duniya, in ji jami'an kasashen waje da kuma kwararru.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, shi ne ya kaddamar da bude gasar wasannin a hukumance da yammacin ranar Juma'a a Wuhan, babban birnin lardin Hubei na kasar.

Adhere Cavince, wani kwararren masanin dangantakar kasa da kasa dan kasar Kenya, wanda ya fi mayar da hankali kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ya bayyana cewa, bikin wasannin ya kara nunawa duniya matsayin kasar Sin cewa bata da niyyar yin amfani da karfin soji wajen cutarwa, ko kuma yiwa wata kasa a duniya barazana a harkokin mu'amallarta da kasa da kasa.

Kasar Masar ta tura tagawa mafi girma a tarihin kasar a gasar ta wannan shekarar a Wuhan.

Birgediya janar Hazim Ali Ibrahim, shugaban sashen wasannin sojojin kasar Masar ya ce, kasar Sin ce ta yi fice a duniya wajen shirye shiryen gasar wasannin, kuma wannan abin yabo ne.

A cewarsa, bikin gasar wasannin sojojin na kasa da kasa wani muhimmin dandali ne da zai baiwa sojojin damar yin wasanni da cudayar al'adu, ya kara da cewa, kasar Masar tana neman kara zurfafa mu'amalar abokantaka ta hanyar gasar wasannin sojojin ta duniya a Wuhan.

Ita dai gasar wasannin sojojin ta duniya wasu jerin wasannin motsa jiki ne a tsakanin dakarun sojoji wanda majalisar shirya wasannin sojoji ta kasa da kasa wato (CISM) ta fara gudanarwa tun a shekarar 1995. Wasannin na wannan shekarar tsakanin ranar 18 zuwa 27 ga watan Oktoba ya janyo hankalin mahalarta wasannin kimanin 10,000 daga kasashen duniya sama da 100.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China