Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji fiye da 9300 za su shiga gasar wasannin sojoji ta duniya karo na 7 a Wuhan
2019-10-18 13:35:45        cri

Za a bude gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7 a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin yau da dare. Yanzu a shirye tsaf domin gudanar da gasar. Sojoji dubu 9 da dari 3 da 8 daga kasashe 109 ne suka yi rajistar shiga gasar. Yanzu sojoji 'yan wasa ciki hada da na kasar Sin suna share fagen yin takara da juna, kuma suna alla-alla a fara gasar mafi girma a tarihi.

Samun bakuncin shirya gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7, mataki ne da kasar Sin ta dauka domin sauke nauyinta a matsayinta wata babbar kasa, da kara azama kan yin mu'amala ta fuskar aikin soja da wasannin motsa jiki, da sa kaimi kan samun zaman lafiya da ci gaba a duniya. Manjo janar Yang Jian, darektan kwamitin zartaswa na gasar ya bayyana a taron manema labaru jiya cewa, yanzu a shirye ake wajen gudanar da gasar yadda ya kamata bayan an dauki shekaru fiye da 2 ana share fage. Ya ce girman gasar da kuma tasirin da za ta yi zai kafa tarihi. Kasar Sin tana kokarin shirya wata kasaitacciyar gasar wasannin sojoji mai ban sha'awa wadda ba a taba ganin irinta a baya ba. "Sojoji dubu 9 da dari 3 da 8 daga kasashe 109 sun yi rajistar shiga gasar, wadanda yawansu ya kafa tarihi. Za su yi takara da juna cikin manyan wasanni 27 masu kunshe da kananan wasanni 329, wadanda yawansu shi ma ya kafa tarihi. Kusoshin rundunonin soja da jama'in ofishin jakadanci dake kula da harkokin soji daga kasashe fiye da 50 za su halarci bikin bude gasar. Gasar za ta yi gagagrumin tasiri."

Yang Jian ya kara da cewa, baya ga yawan sojoji 'yan wasa da ya kafa tarihi, sojoji 'yan wasan za su yi takara sosai da juna a yayin gasar. A cikin sojoji 'yan wasan da suka yi rajistar shiga gasar, akwai wasu 67 da suka taba zama zakaran duniya a baya, wasu 118 da suka kasance matsayi na 8 na farko a gasar wasannin Olympic ta Rio. Ta haka gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa a wannan karo za ta kasance gasar wasannin Olympic ga sojojin kasa da kasa wadda ta dace da sunanta sosai. "Kasashen Rasha, Brazil, Faransa, Jamus, Poland da sauran kasashe 14 sun aika da sojoji 'yan wasa fiye da 100, wadanda suka yi fintikau sosai. Rundunar sojan kasarmu ta Sin ma ta ba gasar muhimmanci. Mun kafa kungiyar 'yan wasa mai kunshe da mutane dari 5 da 53, wadanda yawansu ya kafa tarihi. Yanzu 'yan wasanmu dari 4 da 6 cike suke da kuzari. Suna samun horo na musamman don share fagen gasar, za su rubanya kokari da kuma nuna kuzari cikin gasar don samun maki mai kyau."

Kana, za a gwada halin musamman na kasar Sin a yayin gasar daga dukkan fannoni. Karo na farko ke nan da aka shirya gasar a wurin da ba sansanin soja ba. Haka zalika, karo na farko da aka kafa wani wuri musammam domin 'yan wasa. Kuma karon farko da za a gudanar da baki dayan gasar a birni guda. Darektan kwamitin zartaswa na gasar kuma magajin birnin Wuhan, Zhou Xianwang ya yi karin bayani da cewa, birnin Wuhan yana bin tunanin "gudanar da gasar ba tare da gurbata muhalli da cin hanci ba, wadda ke bude kofa ga kowa da kuma amfanar kowa". Ya samar da filaye da dakunan wasa guda 54, ciki had da sabbabi da kuma na wucin gadi guda 35, yana kuma gudanar da mabambantan ayyukan kyautata muhallin birni, zirga-zirga, hasashen yanayi, tsaron lafiyar al'umma, abinci, ba da magani, karbar baki, masu aikin sa kai da dai sauransu. Mahukuntan Wuhan suna kokarin hada batun shirya gasa da kuma batun raya birnin tare. "Muna fatan kara azama kan ci gaban birninmu ta hanyar shirya gasar. Muna kokarin shirya gasar yadda ya kamata, tare da kawo wa mazauna birninmu alheri mai dogon zango. Sakamakon kyautatuwa da kafa birninmu na tsawon shekaru fiye da 2, ya sa muhallin birninmu da kuma surarsa sun kyautata sosai. Mazauna birninmu sun yi maraba da hakan. Haka kuma suna kara amincewa da birninmu, suna kara alfahari da shi."

An labarta cewa, a karon farko, za a yi amfani da fasahar 5G da 8K da VR wajen watsa shirye-shiryen talibijin yayin gasar, wanda zai kara daga matsayinta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China