Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawara BRI za ta iya taimakawa Afrika cimma ajandarta na sauyi
2019-10-18 11:08:37        cri
An bayyana shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin, a matsayin wadda za ta iya taka gagarumar rawa wajen taimakawa Afrika cimma ajandarta na sauya tsarin tattalin arzikinta.

Michael Chege, shugaban majalisar gudanarwa ta shirin nazarin harkokin tattalin arziki da zamantakewa, na kungiyar kawacen raya nahiyar Afrika NEPAD dake Kenya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, akwai abubuwan da suka yi kamaceceniya da juna tsakanin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da ajandar tarayyar Afrika ta 2063.

Yayin wani taron kan dangantakar Sin da Afrika da Jami'ar Nairobi ta karbi bakuncinsa, Michael Chege, ya ce shawarar ta na iya taka rawa wajen taimakawa Afrika cike gibinta a bangaren ababen more rayuwa.

Ya ce bincike ya nuna cewa, cikin shekaru 18 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ce ta samar da kudin aiwatar da kusan kaso 25 na ayyukan more rayuwa a Afrika, inda aka yi kiyasin gwamnatocin nahiyar sun samar da kaso 40.

Ya ce ya lura cewa, a kowacce shekara, gibin ayyukan more rayuwa a Afrika na kai wa sama da shilling triliyan 10, kwatankwacin dala biliyan 100, kuma shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" za ta iya taimakawa wajen rage wannan gibi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China