Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana kokarin kiyaye wadatar hatsi a duniya a ko da yaushe
2019-10-15 19:51:38        cri

A yau ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya gabatar da wani sharhi mai taken "Sin tana kokarin kiyaye wadatar hatsi a duniya a ko da yaushe". Sharhin ya yi karin bayani kan tsarin da Sin take dauka na samar da isashen hatsi bisa takardar bayanin da gwamnatin kasar ta fitar kan wadatar abinci a kasar Sin a jiya Litinin, matakin da ya bayyana gagarumar gudunmawa da Sin take bayarwa wajen tabbatar da wadatar hatsi da kara hada kai da kasashen duniya wajen samun bunkasuwa na bai daya.

Sharhin ya yi nuni da cewa, jama'ar kasar Sin da yawansa ya kai biliyan 1.4 suna biya bukatun hatsi na dogaro da kansu, ba su kawo wata illa ga duniya ba a wannan fanni, a matsayinta na kasa mai yawan mutane a duniya, Sin ta samarwa mutanenta isashen hatsi gwargwadon karfinta, abin da ya baiwa duniya mamaki matuka.

Kazalika, sharhin ya ce, a matsayinta na kasa dake da mutane da yawansa ya kai kashi 1 cikin 5 na al'ummar duniya, samar da isashen hatsi don dogaro da kanta babbar gudunmawa ce da Sin take bayarwa ga duk duniya baki daya. Amma, Sin ba ta tsaya a wannan ci gaba ba, tana kokarin bude kofarta ga ketare da zurfafa hadin kanta da kasashen duniya don taka rawa gwargwadon karfinta wajen tabbatar da wadatar hatsi a duniya, abin da ya nuna cewa, Sin tana kokarin sauke nauyin dake wuyanta wajen kawar da yunwa a duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China