Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikn waje na kasar Sin ya ci gaba da ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya
2019-10-14 20:10:10        cri

CMG ya fitar da wani sharhi a yau Litinin mai taken "Cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya", inda ya nuna cewa, bana shekaru 70 ke nan da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a cikin wadannan shekarun da suka gabata, Sin ta zama kasa mafi karfi ta fuskar cinikin kayayyaki a duniya daga kasa dake da karancin karfi a wannan fanni, a sa'i daya kuma, ta ba da muhimmiyar gudunmawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Cinikayyar wajen kasar Sin ta samar wa duniya kayayyaki da makamashi masu inganci da arha, a bangaren kayayyakin da ta shigo da su kuwa, kasar Sin ta samarwa duniya wata kasuwa mai girma dake gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Kazalika, bayanin ya nuna cewa, cinikin waje na duniya ya fuskanci koma baya matuka saboda ra'ayin bangaranci da manufar kariyar ciniki, lamarin da ya jawo damuwar hukumomin kasa da kasa sosai. A yayin da cinikin duniya ke fuskantar koma baya, Sin na gudanar da ayyukanta a wannan fanni yadda ya kamata ba tare da wata tangarda ba, abin da ya alamta cewa, cinikayyar wajen kasar Sin na bunkasa cikin inganci kuma na da kyakkyawan tsari da sauya hanyar da take bi cikin sauri, matakin da ya sa ta zama kasa mai muhimmanci wajen tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China