Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya cimma nasarar kai ziyara a Indiya da Nepal
2019-10-13 20:12:11        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aikinsa a kasashe biyu dake kudancin Asiya daga ran 11 zuwa 13 ga wata. Wannan ita ce ziyarar farko da shugaban ya kai kasashen waje tun bayan kammala bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Xi Jinping ya halarci kwarya-kwaryan taron shugabannin Sin da Indiya karo na biyu da aka yi a birnin Chennai, tare kuma da kai ziyarar aiki a Nepal.

Indiya da Nepal makwabtan kasashe ne dake da muhimmanci sosai ga kasar Sin a kudancin Asiya. A shekara mai zuwa ne kuma za'a cika shekaru 70 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Indiya, kana a badin kuma za'a cika shekaru 65 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Nepal. Ci gaban da Xi Jinping ya samu cikin ziyarar a wannan karo, ba ma kawai ya kara amincewa da juna tsakaninsu ba ne, har ma ya zurfafa hadin kai tsakaninsu da cin moriya tare.

Ziyarar shugaba Xi Jinping a wannan karo, ya kawo amfani sosai ga raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma tana da ma'ana sosai wajen sa kaimi ga zaman lafiya da karko da bunkasuwar yankin Asiya da ma duk duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China