Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:Annobar cutar Ebola na samun sassauci a Kongo Kinshasa
2019-10-11 14:38:14        cri

Jami'in hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya bayyana jiya a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa, an samu ci gaba sosai wajen yaki da cutar Ebola a Kongo Kinshasa bisa taimakon kasa da kasa, yana mai cewa, yawan karin mutane da suka kamu da mumunar cutar ya ragu sosai, amma duk da haka, ana bukatar karin kokari don kawar da ita baki daya.

Jami'i mai kula da halin ko ta kwana na WHO Michael Ryan ya bayyana a gun wani taro da aka yi a jiya Alhamis a Geneva cewa, a halin yanzu dai annobar cutar Ebola ta bar birane kuma ta kaura zuwa wasu kauyuka masu nisa. Ya ce ana cimma nasarar yaki da cutar a kasar karkashin kokarin da kasashen duniya suke yi, amma ana bukatar karin kokari don kawar da ita baki daya a kasar, ya ce:

"Kawo yanzu dai, cutar a wannan karo ba ta zo karshe ba tukuna, amma ba za a iya yin hasashe wuraren da mai yiyuwa ne za ta barke nan gaba ba. Na yi imanin cewa, mun riga mun samu nasarar takaita wannan cuta a wasu wurare, yanzu lokacin ya yi da za mu murkushe ta baki daya."

An ba da labari cewa, a watan Afrilu bana lokacin da cutar ta fi addabar mutane, Kongo Kinshasa ta kan samu karin mutanen da suka kamu da cutar kimanin 130 a ko wace rana, kididdigar da aka bayar a makon da ya gabata ta nuna cewa, wannan adadi ya ragu zuwa 20 a kowace rana.

WHO ta fitar da alkaluma cewa, cutar ta kwashe watanni 14 tana addabar wannan kasa, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane fiye da 2100, ciki hadda masu aikin jiyya kimanin 160. A watan Yunin bana, WHO ta ayyana wannan batu a matsayin matsalar dake bukatar daukin kasa da kasa.

Michael Ryan ya ce, hadin kan kungiyar da mahukuntan kasar na taka rawa sosai wajen samun wannan nasara, wannan cuta ta daina yaduwa, kuma ta koma wasu wurare masu nisa kamar lokacin da aka gano ta a watan Agutsta na bara. Wadannan wurare suna da nisa sossai, da wuya ake iya zuwa, domin sai an kwashe awo'i 5 an kuma hau babur kafin a iya kai isa. Ban da wannan kuma, saboda ganin akwai kungiyoyin masu dauke da makamai fiye da 10 a wadannan wurare, da kyar za a iya ba da taimako. Duk da hakan, gwamnatin kasar na kokarin shawarwari da wadannan kungiyoyin don su ajiye bindigoginsu.

Michael Ryan ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, akwai alluran rigakafi iri biyu dake iya tinkarar cutar Ebola, matakin da ya sa yawan mutuwar mutane sakamakon cutar ya ragu matuka. Ya ce:

"Yawan mutuwar mutane saboda wannan cuta ya ragu zuwa kasa da surusi a wasu cibiyoyin jiyya. Duk da cewa yawan mutuwar mutane a duk kasar ya kai kashi 67 cikin dari, yawan mutuwar mutane a cibiyoyin ba da jiyya ya ragu sosai."

Yayin da aka tabo maganar ko cutar ta sake bulla a Tanzaniya, Micheal Ryan ya ce, gwamnatin Tanzaniya ta nanata cewa babu cutar a kasar, WHO kuma za ta ci gaba da dukufa kan ba da taimakon kimiyya ga kasar. Ya ce:

"Gwamnatin Tanzaniya ta nanata cewa, cutar ba ta bullo a kasar ba, kuma sakamakon nazarin da aka yi kan wadanda ake tabbatar ko sun kamu da cutar ya nuna cewa, ba su kamu da ita ba. WHO za ta ci gaba da ba da taimakon kimiyya ga kasar. Tanzaniya ta gabatar da rahoton bayyana mutanen da aka yi tabbatar sun kamu da cuta a makonnin da suka gabata, amma babu wani karin bayani kan kamuwa da sabuwar cuta ko cuta mai tsanani a kasar ba." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China