Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin riko na Sudan ta nada Alkalin alkalai da Atoney Janar a kasar
2019-10-11 10:47:49        cri
Gwamnatin riko na Sudan, ta nada Nemat Abdallah Mohamed Khair a matsayin Alkalin alkalan kasar, yayin da aka ba Taj Al-Sir Al-hebr, mukamin Atoney Janar.

Wata sanarwa ta ruwaito kakakin gwamnatin Mohamed Al-Faki Suleiman na cewa, an yi nadin ne bisa tanadin daftarin kundin tsarin mulki da aka gabatarwa ma'aikatar shari'a ta kasar, wanda kuma aka wallafa a jaridar Gazette ta gwamnatin kasar.

Ya kara da cewa, bayan sun kama aiki, Atoney Janar da alkalin alkalan, za su kafa majalisar kula da harkokin shari'a domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na zaben shugaban majalisar.

Nemat Abdallah Khair, ita ce mace ta farko da zata rike mukamin alkalin alkalai a Sudan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China