Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da yadda jami'an Prague ke tsoma baki kan harkokin cikin gidanta
2019-10-10 19:42:15        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da yadda tun a watan Nuwamban shekarar 2018, manyan jami'an sabon birnin Prague na jamhuriyar Czech ke ci gaba da furta kalaman da ba su dace ba kan manyan batutuwan da suka shafi muhimman muradun kasar Sin, kamar yankin Taiwan da jihar Tibet, matakan da suka saba ka'idojin alakar kasa da kasa, da ma matsayar da al'ummomin kasa da kasa suka cimma.

Ya ce, duk da yadda kasar Sin ta fito fili ta nuna adawa kan wadannan matakai, jawabai, da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da jami'an ke yi, sun shafi alaka da mataki na siyasa da tushen musaya tsakanin biranen kasashen biyu matuka. A saboda haka, birnin Beijing ya sanar da katse alakar abokanta da birnin Prague, da ma dakatar da duk wata musaya a hukumance tsakanin sassan biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China