Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfin gogayyar kasar Sin tana sahun gaba a duniya
2019-10-09 19:41:56        cri

Yau Laraba 9 ga wata gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Karfin gogayyar kasar Sin tana ci gaba da zama a sahun gaba a fadin duniya", inda aka yi nuni da cewa, bisa rahoton karfin gagayyar kasashen duniya na shekarar 2019 da dandalin tattalin arzikin duniya ya fitar yau, karfin gogayyar kasar Sin ya karu da kaso 1.3 bisa dari idan aka kwatanta da bara, amma karfin gogayyar Amurka ya yi kasa warwas, saboda ba ta gudanar da cinikayyar waje yadda ya kamata ba. A halin da ake ciki yanzu, duk da cewa, ana fama da matsalar ba da kariya ga cinikayya da bangaranci, amma karfin gogayyar kasar Sin yana ci gaba da karuwa, lamarin da ya sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin duniya.

Sharhin ya jaddada cewa, dalilin da ya sa karfin goggayar kasar Sin ya karu shi ne domin kasar Sin tana da babbar kasuwa, haka kuma tana samun ci gaban tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare, kana karuwar karfin kirkire-kirkire ita ma tana ingiza karuwar karfin goyayyar kasar Sin a fadin duniya. Rahoton karfin gagayyar kasashen duniya na shekarar 2019 ya nuna cewa, alkaluman kasuwar kasar Sin sun kai maki 100 wanda ya kai matsayin koli a duniya, alkaluman karfin tattalin arzikin kasar Sin sun kai maki 98.8, kana karfin kirkire-kirkiren kasar Sin ya kai matsayi na 24 a duniya, kana karfin kirkire-kirkiren kasar a bangaren nazari da raya kimiyya da fasaha yana cikin kasashe goma wadanda suke sahun gaba a duniya, yanzu haka gwamnatin kasar Sin tana ci gaba da nacewa kan manufar bude kofa ga kasashen ketare domin cimma burin raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, ko shakka babu kasar Sin tana kara kokari matuka domin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China