Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karuwar sayayya na ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin
2019-10-08 19:12:07        cri

Yau Talata 8 ga wata gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Karuwar sayayya tana ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin", inda aka yi nuni da cewa, yayin da aka yi bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar kasar Sin tsakanin ranekun 1 zuwa 7 ga wannan wata, gaba daya adadin kudin da aka kashe a bangaren yawon shakataka a cikin gidan kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 649.71, a bayyane ana iya lura cewa, yadda ake kara kashe kudi yana ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, duk da cewa, tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma ana fama da matsalar ra'ayin ba da kariya ga cinikayya da bangaranci, amma tattalin arzikin kasar Sin yana gudana cikin lumana, dalilin da ya sa haka shi ne domin kudin da Sinawa suke kashewa a yau da kullum yana kara karuwa.

Sharhin ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2018, karuwar sayayya tana ci gaba da taka rawar gani a fannin ingiza karuwar tattalin arzikin kasar Sin a cikin shekaru 5 da suka gabata, a cikin watanni shida na farkon bana, karuwar sayayya tana ba da gudummowa wajen karuwar tattalin arzikin kasar da ya kai kaso 60 bisa dari, al'ummun kasar suna jin dadin sayen kayayyaki masu inganci da kamfanonin kasar suke samarwa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China