Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin na gaggauta bunkasuwar sha'anin fasahar zamani a Afrika
2019-10-08 14:40:32        cri

Nahiyar Afrika mai fadin yankuna na da makoma mai haske matuka a fannin fasahar zamani ta digit, wannan zamani da muke ciki na yanar gizo na canja salon rayuwar 'yan Afrika. Salular da kamfanin Sin ta kera dake amfani da harshen Rwanda, da kuma salular dake amfani da kimiyyar zamani da Afrika ke saye daga kasar Sin na cika kasuwar nahiyar, abubuwan dake alamta cewa, kamfanin Sin na ba da gudunmawarsa wajen gaggauta bunkasuwar fasahar zamani a nahiyar.

Shugaban kungiyar Sinawa dake Rwanda Yin Qingri ya gabatar da wani rahoto a shafinsa na sada zumunta na WeChat, wanda ya bayyana yadda ya gabatarwa shugaban kasar Rwanda Paul Kagame wata salula mai launin baki, salula ta farko dake amfani da harshen Rwanda a duniya, wadda kamfanin Yin Qingri ya kera ta. Yin Ya ce:

"Da isowarmu a kasar Rwanda, mun gano cewa, jama'ar kasar ba su san harsunan Ingilishi ko Faransanci ba sai harshen Rwanda, a wannan lokaci kuma, salula wata sabuwar kaya ce, ana iya sarrafa ta ne da Ingilishi ko Faransanci kawai."

A shekarar 2007, salula ta farko dake amfani da harshen Rwanda ta bullo, wadda ta samu jinjina matuka daga shugaban kasar Paul Kagame, tare da samun karbuwa sosai a kasar.

Ya zuwa yanzu, salula ta zama wani muhimmin bangare na zaman rayuwar jama'a a Afrika, nahiyar Afrika dake da yawan mutane fiye da biliyan 1.2, ta zama wata babbar kasuwa dake samun saurin bunkasuwa, tamburorin kasar Sin na ba da muhimmiyar rawa wajen raya wannan kasuwa. Kamfanin Tecno ya yi suna sosai a wannan fanni. Wannan tamburi dake mai da hankali a ketare, an yi masa lakabi da "Sarkin salula" a Afrika.

Kowa ya san Tecno a Afrika, wadda ta fara aikinta a nahiyar daga shekarar 2008, kuma ta kasance daya daga cikin tambura na farko daga kasar Sin da suka shiga kasuwar Afrika. Wang Chong, Manajan kamfanin na Yankin gabashin Afrika, wanda kuma ke cikin jami'an sayar da salula na farko da suka bude kasuwa a Afrika, ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata, sun yi kokarin gwagwarmaya don habaka wannan kasuwa. Ya yi waiwaye cewa, tamburan kasa da kasa da dama sun shiga wannan kasuwa, amma suna mai da hankali kan kasuwar duniya, hakan ya sa suka kasance koma baya wajen biyan bukatun 'yan Afrika, wanda ya zama wata babbar dama ga kamfanonin kasar Sin. Ya ce:

"Bayan nazarin da muka yi a nahiyar, mun gano bukatar bullo da wata salula dake biya bukatun 'yan Afrika. Wannan kasuwa a shekaru 10 da suka gabata, na da boyayyen karfi matuka, matakin da ya ba mu dama mai kyau wajen bude wannan kasuwa mai tasowa."

Wang Chong ya shedawa manema labarai cewa, Tecno ya bullo da salula dake iya biyan bukatun 'yan Afrika, alal misali kyamarar da ta dace da bukatun bakaken fata, harsunan Afrika, yin aiki cikin dogon lokaci bayan an yi caji, salula dake dauke da salon wake-wake irin na Afrika, salula dake iya daukar katin sim biyu ko hudu.

Kididdigar da aka bayar na nuna cewa, yawan salula da Tecno ta sayar ya kai miliyan 124, wanda ya kai kashi 48 cikin dari na dukkanin kasuwar Afrika. Rahoton da cibiyar tattara alkaluman yanar gizo ta bayar, na nuna cewa, Tecno ta kai matsayin farko a fannin salula na zamani a shekarar 2018. A sa'i daya kuma, tamburan kasar Sin da dama sun shiga wannan kasuwa, wato Huawei, MI da OPPO da sauransu, wadanda kuma suke da kaso mafi yawa a wannan kasuwa, hakan ya sa Sin ta kai matsayin farko na shigar da salula Afrika.

A hannu gudu kuma, ban da kokarin inganta injunansu, kamfanonin Tecno da Startimes suna kokarin bullo da wasu kayayyaki kan yanar gizo wato kide-kide, injunan wasa da bidiyoyi da sauransu, matakin da ya gaggauta bunkasuwar fasahar zamani a nahiyar Afirka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China