Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana kimiyya guda uku sun samu lambobin yabo na Nobel ta shekarar 2019
2019-10-08 10:27:25        cri

Cibiyar nazarin ilmin likitanci na Karolinska ta kasar Sweden, ta bayar da sanarwa a jiya Litinin, inda ta ce ta ba masana kimiyya guda uku, ciki har da William G. Kaelin da Gregg L. Semenza na kasar Amurka, da Peter J. Ratcliffe na kasar Burtaniya lambobin yabo na ilmin yadda jikin halittu ke aiki da na likitanci ta shekarar 2019, don yaba musu kan rawar da suke takawa a fannin nazarin yadda kwayoyin halitta ke samu da dacewa da yadda ake samar da iskar Oxygen.

Kwamitin nazarin ba da lambobin yabon ya jaddada cewa, nasarorin da aka cimma a fannin a shekarar da muke ciki, ya "ba da hanya da ta dace wajen gano sabbin dabarun tinkarar cutar karancin jini da sanakara da kuma sauran cututtuka". (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China