Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar kiyaye muhalli ta Sin ta inganta aikin kiyaye muhallin duniya
2019-10-07 16:01:39        cri
Tun daga shekarar 2000 zuwa 2017, yawan itatuwan da kasar Sin ta kara shukawa ya kai fiye da kashi 1 cikin 4 na adadin da aka kara shukawa a duniya, wanda ya kasance a matsayin farko a duniya. Sin ta samu nasarori wajen kyautata muhalli da samun ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba saboda yadda gwamnatin kasa ta tsara manufofi da kara sa ido da yadda ake kula da harkokin kiyaye muhalli, da yadda Sinawa da dama ke kara shiga aikin kiyaye muhalli. Sinawa su kan ce, "kyakkyawan muhalli yana haifar da moriya".

Sharhin ya jaddada cewa, sauyin yanayi kalubale ne da dukkan dan Adam ke fuskanta, don haka, akwai bukatar dukkan kasashen duniya su shiga aikin kiyaye muhalli. A gun taron kolin MDD kan batun sauyin yanayi da aka gudanar a karshen watan Satumba, Sin ta bayyana cewa, za ta aiwatar da yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi na MDD da yarjejeniyar Paris, kana ta jaddada cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka kan ra'ayin bangarori daban daban don tinkarar sauyin yanayi, da martaba ka'idojin daukar alhaki tare bisa la'akari da bambanci dake tsakanin kasashe. Sin ta kara yin alkawarin tinkarar sauyin yanayi ga kasa da kasa, tare da gabatar da ra'ayoyinta kan tafiyar da yanayin muhallin duniya, wannan ya shaida alhakinta da imaninta a wannan fanni. Sin za ta kasance muhimmiyar kasa mai shiga da samar da gudummawa da bada jagoranci ga aikin kiyaye muhallin duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China