Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na son ci gaba da tattaunawa da DPRK bayan tattaunawar Stockholm ta ci tura
2019-10-06 16:47:45        cri

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Asabar cewa, wakilanta sun yi kyakkyawar tattaunawa da takwarorinsu na Koriya ta Arewa (DPRK) a shirin tattaunawar baya bayan nan da ya gudana a Stockholm, babban birnin kasar Sweden.

Ana sa ran sake dawowa kan teburin tattaunawar nan da makonni biyu masu zuwa, duk da cewa Pyongyang ta ce tattauanwar ta ci tura sakamakon tufka da warwarar da Washington ke yi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurkar Morgan Ortagus, ya yi tsokaci 'yan sa'o'i kadan bayan da babban jami'in tattaunawar DPRK, Kim Myong Gil, ya yi tattaunawar sa'o'i 8 da rabi tare da wakilan bangaren Amurka, ya bayyanawa manema labarai cewa, shirin tattaunawar nukiliyar zirin Koriya ya rushe.

Sai dai kalaman Ortagus, ya ci karo da tsokacin Kim, wanda ya ce Amurka ta kawo shawara mai kyau kuma ta yi kyakkyawar tattaunawa da takwarorinta na DPRK.

Babu tabbas ko Pyongyang ta amince za ta sake ganawa da wakilan Amurkar nan da makonni masu zuwa a birnin Stockholm.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China