Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Benin zai halarci taron UEMOA
2019-10-03 15:41:53        cri

Shugaban kasar Benin Patrice Talon, zai halarci taron tsaron harkokin kudi da babban kwamitin kungiyar tattalin arziki da harkokin kudi na kasashen yammacin Afirka (UEMOA) ke shiryawa.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta bayyana cewa, taron na yau, wani bangaren na bitar yanayin tsaro da ake fuskanta a kasashen kungiyar 8, wato Benin, Burkina-Faso, Ivory Coast, da Guinea-Bissau, da Mali, da Nijar, da Senegal da kuma Togo.

A 'yan shekarun nan, kasashen na UEMOA sun yi fama da ayyukan ta'addanci, musamman kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da Ivory Coast.

Baya ga tsattauran ra'ayin addini, da 'yan fashin teku, da almundahanan kudade, matsaloli na lafiya da muhalli, miyagun kwayoyi, faraucin makamai da na bil-Adama na daga cikin abubuwan dake damun kasashen, kuma sun kasance babbar barazana ga tsaron rayuka da kadarori a shiyyar.

An kafa kungiyar ta UEMOA ce a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 1994 a Dakar na kasar Senegal, da nufin gudanar da harkokin tattalin arziki tsakanin iyakokin kasashen dake amfani da kudaden CFA. Yanzu haka dai kasashe 14 a yammaci da tsakiyar Afirka ne ke amfani da takardar kudin CFA a matsayi na bai daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China