Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za'a shirya taron nahiyar Afrika don tattauna batun yaki da rashawa
2019-10-02 15:15:33        cri

Hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD ta sanar cewa, a wata mai zuwa, kungiyar tarayyar Afrika (AU), da bankin raya ci gaban Afrika (AfDB), da kuma hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), za su shirya wani babban taro game da matakan da za'a bi wajen yaki da ayyukan rashawa a bangaren filaye na kasashen Afrika.

Taron game da batun tsara manufofin filaye a Afrika (CLPA-2019), wanda zai gudana tsakanin ranar 25 zuwa 29 ga watan Nuwamba mai taken "Neman cimma nasarar yaki da rashawa a fannin filaye: Hanyar samun dawwamamman ci gaban Afrika," cibiyar tsara filaye ta Afrika (ALPC) ta shirya taron, tare da hadin gwiwar hukumar AU, da ECA, da kuma AfDB.

ECA ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar jiya Talata cewa, babban taron zai kasance tamkar wani muhimmin tsari ne da ba da damar nazartar al'amurran da suka shafi yadda za'a zurfafa manufofin inganta tsarin filaye a Afrika ta hanyar samun muhimman bayanai da karin ilmi game da aiwatar da shirin bunkasa filaye na nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China