Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ci gaban Sin da gudummawar ta ga duniya bayan shekaru 70 da kafuwar janhuriyar kasar
2019-10-01 18:24:22        cri

Yayin da ake ci gaba da bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, hankulan manazarta da masu fashin baki na kan irin ci gaba da kasar ta samu cikin wadannan shekaru.

Zai yi wuya cikin kananan jumloli, a iya fayyace wadannan tarin nasarori, amma idan abun a takaita ne, cikin sauki ana iya bayyana irin kwazon mahukuntan kasar karkashin JKS wajen tsarawa, da aiwatar da manufofin tattalin arziki masu halayyar musamman na Sin, wadanda sanadiyyarsu, kasar ta kai ga zama ta biyu a duniya a fannin karfin tattalin arziki, tare da tsame miliyoyin al'ummarta daga kangin talauci.

Wani abun sha'awa shi ne, yadda kasar Sin ke daukar matakai na bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Wannan buri tamkar manuniya ce dake tabbatar da babban burin bil Adama, na rayuwa cikin kyakkyawan muhalli mai nagarta.

Bugu da kari, kasar Sin ta cimma nasarori a fannonin amfani da yawan al'ummar ta, wajen kafa kasa mai matsakaiciyar wadata da kowa zai yi alfahari da ita. Sin ta dage wajen dinke dukkanin wata baraka da ka iya yin barazana ga kasancewar ta daya tak a duniya. Mahukuntan ta na ci gaba da aiwatar da matakan diflomisiyya da hadin gwiwa da sauran sassa na duniya, ba tare da nuna wata wariya ba, burin dai bai wuce cin gajiya tare da sauran kasashe duniya ba, musamman kasashe masu tasowa ciki hadda nahiyar Afirka, wadda ke matsayin babbar kawa, kuma aminiya ga kasar Sin, duka dai domin a gudu tare a tsira tare.

Da dukkanin wadanda suka ganewa idanun su ci gaban da kasar Sin ta samu, a bayyana take cewa, raya harkar ilimi ta taka muhimmiyar rawa, wajen tsara managartan manufofin ci gaban Sin. Kasar Sin ta kuma habaka harkokin noma, da binciken kimiyya da Fasaha, da ayyukan kere kere. Ta raya masana'antu da harkokin sufuri, da sauran ababen more rayuwa, ta yadda dukkanin sassan duniya ke jin amon ta a duk wata harka ta ci gaban rayuwar bil Adama.

Karbuwar da kasar Sin ta samu a fannin hadin gwiwa da kasashen waje, ta bata damar yin ingantaccen kawance, da aminci tsakanin ta da dukkanin nahiyo. Sai dai a hannu guda hakan ya sa wasu kasashe musamman na yammacin duniya, sun rika nuna mata yatsa, tare da zargin ta da aikata wasu laifuka ta hanyar kage da boye gaskiya. Amma dai ko ba komai, gudummawar da kasar Sin ke ci gaba da samarwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, na tabbatar da karbuwa da inganci, da kuma karkon manufofin ta na bunkasuwa, lamarin da ke zama abun koyi ga dukkanin kasashen dake fatan bin hanya mai bullewa

Yayin kasaitaccen biki da babban direktan kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin soja Xi Jinping ya jagoranta a yau Talata 1 ga watan Oktoba domin ciki shekaru 70 da kafuwar janhuriyar al'ummar Sin, an gudanar da babban faretin soja, mai kunshe da sojoji dubu 15, da maci na mutane da yawansu ya kai dubu 100.

Ko shakka ba bu, ana iya cewa kasar Sin ta cimma manyan nasarori da duniya ba za ta taba mantawa da su ba, musamman ganin kasar ita da kan ta, ta zabawa kan ta makoma ko tafarki mafi dacewa da yanayin al'ummar ta, da salon mulki mai cikakken 'yanci, abun koyi ga sauran sassan na duniya.

Bayan shan bukukuwa, fatan da kowa ke yi shi ne ci gaba da dorewar bunkasuwar kasar Sin, kasancewar hakan zai haifar da karin ci gaba cikin hadin gwiwa tsakanin ta da sauran sassan duniya, kamar dai yadda mahukuntan ta suka sha nana ta wannan aniya! (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China