Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da "kantar littattafan Sinanci" a Afirka
2019-10-08 09:13:14        cri

A ranar 25 ga watan Satumba, aka bude bikin nune-nunen littattafai na kasa da kasa karo na 22 na birnin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya. A wannan rana, tawagar wakilan aikin dab'i ta kasar Sin ta yi bikin kulla yarjejeniyar hadin gwiwar ta "kantar littattafan Sinanci" a kasar Kenya, watau bikin nune-nunen ayyyukan madaba'ar lardin Hubei na kasar Sin. Haka kuma, an riga an kaddamar da shirin "kantar littattafan Sinanci" a kasashe da dama da suka hada da kasashen Cuba, da Thailand, da Jamus, da Iran da kuma kasar Canada da sauransu, domin gabatar da littattafan Sin masu ma'ana ga mutanen kasa da kasa, kana, wannan shi ne karo na farko da aka kaddamar da shirin a nahiyar Afirka.

Ga karin bayanin da Maryam Yang ta hada mana:

"Kantar littattafan Sinanci" yana kunshe da littattafai sama da iri dari 5, kamar littattafan koyon Sinanci, da na yara, da na al'adun al'ummomin Sinawa da na kimiyya da fasaha da dai sauransu, kuma an fassara galibi daga cikinsu zuwa harshen Turanci, domin 'yan kasar Kenya su iya karantawa, musamman ma yaran kasar Kenya. Ban da haka kuma, akwai wasu litattafai na Sinanci da na harshen Kiswahili. Babban manajan kamfanin yada labaru da al'adu na Enjoy Yang Yunpeng ya bayyana cewa, "Bana, an kaddamar da shirin kantar littattafan kasar Sin a wurare guda biyu na kasar Kenya, watau babban laburaren kasa na Kenya da kuma jami'ar Nairobi. An samar da wasu littattafai ga mazauna wuri, wasu kuma ana sayarwa, ciki har da littattafai na harsuna da na yara da sauransu. A nan gaba kuma, za a bude sabbin kantunan littattafai a hamshakiyar kasuwa, yankin ciniki na babban laburaren kasar Kenya, da sabuwar makarantar kwalejin Confucius ta jami'ar Nairobi."

Mataimakiyar shugaban Madaba'ar Changjiang na lardin Hubei Bi Hua ta bayyana cewa, musayar al'adu muhimmin batu ne tsakanin musayar dake tsakanin kasar Sin da kasar Kenya, har da da kasashen Afirka baki daya. Mazauna wurin da dama sun gaya mata cewa, littattafan Sin suna samun karbuwa sosai a kasar. Ta ce, "Muna jin dadi kwarai da gaske don ganin mutanen Sin suna son littattafan game da kasar Kenya, kuma 'yan kasar Kenya suna sa ran kara fahimtar harkokin Sin, shi ya sa, musayar al'adu dake tsakanin bangarorin biyu za ta samu ci gaba."

Cikin bikin kulla yarjejeniyar da aka yi a wannan rana, jami'ar Nairobi da kamfanin yada labaru da al'adu na Enjoy, da babban laburaren kasar Kenya da kamfanin yada labaru da al'adu na Changjiang na lardin Hubei sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa ta samar da "kantar littattafan Sinanci" da "kantar littattafai na Jingchu". Makadashin shugaban jami'ar Nairobi Isaac Mbeche ya yaba matuka da ganin kamfanin yada labaru da al'adu na Changjiang ya shiga cikin kasar Kenya, har ma da kasashen Afirka baki daya, ya kuma taya murnar kaddamar da "kantar littattafan Sinanci" a nahiyar Afirka karo na farko. Ya ce, muna fatan samun karin kamfanonin wallafa littattafai da kayayyakin al'adun Sin da Afirka a Afirka, domin zurfafa musayar al'adu dake tsakanin jama'ar Sin da Afirka. Ya kara da cewa, "Yarjejeniyoyin da aka kulla a yau za su raya harkokin karatu da yada labarai a kasar Kenya. Hadin gwiwar dake tsakanin shirin "kantar littattafan Sinanci" da kwalejin Confucius na jami'ar Nairobi za ta kara irin littattafanmu, da zai samar da karin damammakin karanta su ga daliban kasar Kenya. "

A nata bangare kuma, mataimakiyar shugaban babban laburaren kasar Kenya Wangari Ngovi ta ce, an kaddamar da shirin "kantar littattafan Sinanci" karo na farko a Afirka, wanda zai zurfafa mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da Kenya, da kuma kara musayar dake tsakanin mutanen kasashen biyu. Tana mai cewa, "Muna bukatar musayar al'adu kwarai da gaske, da kuma kara fahimtar al'adun al'ummomin Sinawa. Shi ya sa, muke godiya matuka domin littattafan da Sin ta samar mana bisa shirin "kantar littattafan Sinnaci", muna fatan Sin da Kenya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar al'adu dake tsakaninsu."

Bugu da kari, mashawarcin jakadan Sin dake kasar Kenya Wang Xuezheng ya bayyana cewa, hadin gwiwa ta wannan karo za ta habaka musayar al'adu dake tsakanin al'umomin kasar Sin da kasar Kenya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China