Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana ta kara kuzari wajen daidaita sauyin yanayi a duniya
2019-09-24 20:34:15        cri

Jiya Litinin 23 ga wata ne MDD ta bude taron kolin ayyukan daidaita sauyin yanayi a hedkwatarta dake birnin New York na kasar Amurka, a kokarin kara azama kan daukar manyan matakan tattalin arziki wajen daidaita matsalar sauyin yanayi.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda kuma shi ne wakilin musamman na shugaban kasar Sin ya bayyana a yayin taron cewa, kasar Sin za ta sauke nauyin da aka dora mata bisa "yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi", da "yarjejeniyar Paris", za ta kuma tabbatar da manufarta game da daidaita matsalar sauyin yanayi, a daidai lokacin da aka tsara. Har ila kasar za ta sake yin alkawari a gaban kasashen duniya, dangane da daidaita matsalar sauyin bayanin, ta kuma nuna aniyarta game da hakan, kana ta sauke nauyinta yadda ya kamata.

Yanzu haka dai an shiga muhimmin matakin daidaita sauyin yanayi a duniya, don haka kamata ya yi kasashen duniya su sauke nauyi yadda ya kamata, su nuna aniya, su dauki matakai, su kuma hada kai cikin sahihanci wajen tinkarar kalubalen tare. Kaza lika su kuma kara azama kan aiwatar da "yarjejeniyar Paris" daga dukkan fannoni yadda ya kamata, a kokarin kara sabon kuzari na tinkarar sauyin yanayi.

Ko shakka babu, kasar Sin wadda ke tsayawa kan raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, za ta kara kuzari a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China