Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na shugaban Sin ya halarci taron koli na tinkarar sauyin yanayi na MDD
2019-09-24 13:40:35        cri


Jiya Litinin, an kira taron koli kan matakan tinkarar sauyin yanayi a hedkwatar MDD dake birnin New York. Manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci taron tare da ba da jawabi mai taken "Hadin kai wajen tinkarar sauyin yanayi da raya halittun duniya bai daya". Babban sakataren MDD Antonio Guterres shi ne ya jagoranci taron.

A cikin jawabinsa, Wang Yi ya ce, a halin yanzu, duniya baki daya na fuskantar sauyin yanayi, kamata ya yi a hada kai domin tinkarar wannan matsala tare, wanda ke da alaka sosai da makomar Bil Adama. Wang Yi ya nuna cewa, a halin yanzu, an shiga wani muhimmin mataki na magance matsalar sauyin yanayin duniya. Ya kamata, kasashen duniya su nace ga daukar hanyar da ta dace wajen tinkarar sauyin yanayi tare da daukar matakan da suka dace. Ya ce:

"Dole ne mu nuna imani da kwarin gwiwa wajen samun nasarar tinkarar sauyin yanayi. Kuma mu cika alkawari da tabbatar da matsaya daya da muka cimma a yarjejeniyar Paris, da kokarin samun ci gaba a taro karo na 25 na kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi na MDD, ta yadda za a ba da gudunmawa wajen gaggauta aikin tinkarar sauyin yanayi nan da shekarar 2020 tsakanin kasashe daban-daban. Babu wani abin da zai canja tunanin kasashen duniya a wannan fanni, duk da cewa, wasu kasashe sun janye daga cikin yarjejeniyar. Ya kamata mu rika daukar matakai da suka dace ba tare da bata lokaci ba a wannan fanni. Sannan kuma, mu hada aikin tinkarar sauyin yanayi da ciyar da al'umma waje guda, wato samun bunkasuwa mai sauri tare da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, matakin da zai ba mu damar magance sauyin yanayi cikin dogon lokaci. A hannu guda kuma, kamata ya yi mu hada kai bisa sahihiyar zuciya da nacewa ga gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, musamman ma tsayawa tsayin daka kan ka'idar daukar nauyin baki daya tare bisa la'akari da bambancin dake tsakaninmu da dai sauransu, kana da mutunta halin da kasashe masu tasowa ke ciki da taimakawa wadannan kasashe wajen kara karfinsu a wannan fannni. Ya zama wajibi ga kasashe masu wadata su cika alkawarinsu na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da samar da dala biliyan 100 a ko wace shekara nan da shekarar 2020. "

Wang Yi ya kara da cewa, Sin za ta cika alkawarinta tare da daukar matakan da suka dace, don taka rawarta yadda ya kamata wajen tinkarar sauyin yanayi. Ya ce:

"Sin na bin hanyar raya tattalin arzikinta tare da kiyaye muhalli, ta kuma lashi takobin nacewa ga wannan hanya. Sin za ta sauke nauyin dake wuyanta wajen aiwatar da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta MDD da yarjejeniyar Paris, alal misali, gabatarwa ofishin sakataren MDD gudunmawar da Sin za ta bayar nan gaba. Ban da wannan kuma, Sin za ta nace ga hada kai da sauran kasashe don samun bunkasuwa mai dorewa tare da amfani da dandalin kasa da kasa na samun bunkasuwa mai dorewa karkashin shawarar 'ziri daya da hanya daya,' da dai sauransu, matakin da zai taimaka wajen kara hadin kan kasa da kasa a wannan fanni."

Dadin dadawa, Wang Yi ya ce, Sin na dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhalli. A matsayinta na jerin kasashe masu ba da jagoranci ga shirin warware matsalar sauyin yanayi bisa tushen halittu, Sin ta hada kai da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, wajen gabatar da shawarwari guda 150, da gabatar da abubuwan koyi fiye da 30 a wannan fanni. Matakin da ya samar da sabbin hanyoyi wajen zurfafa fahimtar dangantakar dake tsakanin Bil Adama da halittu, kuma ya gabatar da sabbin matakan tinkarar sauyin yanayi da ba da goyon baya mai inganci wajen cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa nan gaba.

Wang Yi ya kara da cewa, Sin ba za ta canja matsayinta na tinkarar sauyen yanayi ba, duk da cewa yanayin da duniya ke ciki yana yin manyan sauye-sauye a halin yanzu, kuma za ta nace ga hadin kai da sauran kasashe da ba da gudunmawarta wajen sa kaimi ga daidaita matsalar sauyin yanayi tsakanin kasa da kasa. Ya ce:  

"Ana fuskantar kalubaloli da matsaloli masu dimbin yawa wajen tinkarar sauyin yanayi, amma 'kowa ya yi da kyau zai ga da kyau'. Ko shakka babu, za a iya cimma muradun samun bunkasuwa mai wadata cikin hadin kai ba tare da gurbata muhalli ba."(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China