Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Shekarar 2015 zuwa 2019 za su zama shekaru mafiya zafi a tarihi
2019-09-23 15:46:11        cri

Wani rahoto da MDD ta fitar a jiya Lahadi na nuna cewa, shekarar 2015 zuwa 2019 za su zama shekaru mafiya zafi a cikin tarihin bil Adama.

Za a mikawa taron koli yaki da matsalar sauyin yanayi na MDD wannan rahoto mai taken "Hadin kai ta fuskar kimiyya", rahoton da ya bayyana muhimmanci da gibin dake tsakanin muradun da bangarori daban-daban suka cimma da kuma halin da muke ciki yanzu kan matakan tinkarar sauyin yanayi.

Ban da wannan kuma, rahoton ya nanata cewa, idan kasashen duniya ba su dauki matakan da suka dace tare da ba da gudunmawarsu yadda ya kamata ba, ba za a kaucewa karuwar yanayin zafi da zai kai sama da makin digiri 1.5 na ma'aunin celcius ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China