Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin dake Kongo Kinshasa ta mika ikon ba da jagora karo na 22
2019-09-23 10:42:02        cri

Jiya Lahadi, sojoji injiniyoyi na kasar Sin dake Kongo Kinshasa da tawagar ma'aikatan lafiya, suka mika jagorar aiki, matakin dake nuna cewa, rukuni na 23 na rundunar kiyaye zaman lafiya ya maye gurbin na 22, tare da fara wa'adin aikinsa na shekara daya.

Sabon rukunin sojoji injiniyoyi na matakin farko a wannan karo sun hada da sojoji 90 da masu aikin jiyya 20, kuma karon farko da kasar Sin ta yi tura tare da jigilar sojojin kiyayen zaman lafiya ta jiragen saman soja zuwa Kongo Kinshasa, matakin da ya gwada karfin jiragen sojin kasar Sin na yin jigilar dogon zango.

Rukuni sojojin na 22 sun kammala aikinsa da kyau na wa'adin shekara daya, kuma dukkan sojoji sun samu lambar yabo ta zaman lafiya daga MDD, kuma za su dawo kasar Sin rukuni-rukuni kamar yadda aka tsayar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China