Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarar "ziri daya da hanya daya" na taimakawa hadin-gwiwar Sin da kungiyar ASEAN
2019-09-20 16:21:54        cri

Za'a kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin Sin da na kungiyar ASEAN wato kungiyar hadin-kan kasashen gabashi da kudancin nahiyar Asiya gobe Asabar a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kasar Sin. Gidan rediyon kasar Sin CRI ya gabatar da wani sharhi game da bikin, inda ya nuna cewa, a yayin bikin, bangarorin biyu za su kulla wasu yarjeniyoyin hadin-gwiwa game da cinikayya da zuba jari da gine-gine da jigilar kaya da sauransu.

Sharhin ya jaddada cewa, bikin baje-kolin wani muhimmin dandali ne tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN wajen yin mu'amala da hadin-gwiwa. A halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen kimiyya da fasaha da masana'antu a duniya, kana kuma ra'ayin nuna bangaranci da na ba da kariya na kara yin barazana ga ci gaban harkokin kasa da kasa. Fadada hadin-gwiwar Sin da kungiyar ASEAN a fannonin tattalin arziki da kasuwanci na da babbar ma'ana, al'amarin da zai taimaka sosai ga bunkasuwar bangarorin biyu, da sanya sabon kuzari ga ci gaban yankin Asiya da na tekun Pasifik.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China