Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya
2019-09-20 10:14:32        cri

Farashin mai ya yi tashin gauron zabo jiya a kasuwannin duniya, yayin da ake nuna damuwa game da yiwuwar fuskantar karancinsa.

Sai dai ministan makamashi na kasar Saudiya Abdulaziz bin Salman, ya bayyana cewa, za a dawo da yadda ake samar da man nan da karshen watan Satumba. Masu sharhi na cewa, masu zuba jari na nuna damuwa kan yadda ake fuskantar karanci man a duniya, da ma yadda hakan ka iya shafar farashinsa a kasuwa.

A karshen makon da ya gabata ne dai, wasu jirage marasa matuka, suka kai hari kan manyan matatun man kasar Saudiya, inda suka lalata gangunan danyen mai miliyan 5.7 da ake hakowa a ko wace rana. Adadin da ya kai rabin man da kasar take hakowa ko sama da kaso 5 cikin 100 na adadin man da ake hakowa a duniya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China