Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matan Sin na bayar da gudummawa ta musamman ga sha'anin matan duniya
2019-09-19 20:33:29        cri

Yau Alhamis gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken "Daidaito, ci gaba da amfana tare: Ci gaban gwagwarmayar mata a cikin shekaru 70, bayan kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin". Inda aka yi bayani kan yadda matan Sin ke aiwatar da hakkokinsu na demokuradiyya, da sa hannu cikin bunkasar tattalin arziki, da ma more sakamakon gyare-gyare da ci gaban kasar cikin adalci, a fannonin sa hannu cikin harkokin siyasa, da samun ilmi, da lafiyar jiki, da ba su tabbacin zaman rayuwa, gina gida, da ma cudanya tare da kasashen duniya. Takardar dai ta nuna babbar gudummawar da matan Sin ke bayarwa, a sha'anin mata na duk fadin duniya.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, tabbatar da matsayi da hakkin mata na kasar Sin, ya sa kaimi gare su wajen bunkasa zamantakewar al'ummar kasar. A halin yanzu, yawan matan da suka yi aiki a kasar Sin, ya kai fiye da 4 cikin goma a dukkan sana'o'i.

'Yar sama jannati ta farko ta kasar Sin Liu Yang, da kwararriyar farko ta Sin da ta samu lambar yabo ta Nobel Tu Youyou, da kuma mata 8 dake cikin jerin sunayen mutane 42 da suka samu lambobin yabo na kasar Sin, dukkansu sun shaida cewa, mata sun samar da gudummawa wajen bunkasa kasar Sin.

Marigayi tsohon shugaban kasar Sin Mao Tsedong ya taba yabawa matan kasar Sin da cewa, suna taka muhimmiyar rawa a zamantakewar al'ummar kasar. Bisa rahoton da cibiyar bincike ta McKinsey ya gabatar a shekarar 2017, an ce, yawan GDP da mata ke samarwa a kasar Sin ya kai kashi 41 cikin dari, wanda ya zama matsayin koli a dukkan yankunan duniya.(Kande, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China