Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon shugaban babban taron MDD: Sin tana kara taka rawa kan dandalin kasa da kasa
2019-09-18 19:49:07        cri

A ranar 17 ga wata sabon shugaban babban taron MDD Tijani Mohammed Bandi, ya zanta da manema labaran kafofin watsa labaran kasar Sin, a hedkwatar MDD dake New York, inda ya bayyana cewa, tun bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, kasar Sin ta fara taka rawar gani a dandalin kasa da kasa, haka kuma za ta kara ba da gudummowa a nan gaba.

Mohammed Bandi ya kara da cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, kasar Sin tana matukar kokari, domin kubutar da kanta daga kangin talauci, har ta kai ga zama babbar kasa wadda ke taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya, musamman ma tattalin arzikin kasashe masu tasowa. Ya ce ana iya cewa, kasar Sin tana ba da babbar gudummowa ga ci gaban bil Adama.

Mohammed Bandi yana ganin cewa, ba ma kawai kasar Sin ta cimma burim kubutar da al'ummun kasarta sama da miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru sama da goma kawai ba, har ma za ta cimma burin kawar talauci daga dukkan fannoni, a cikin wannan babbar kasa mafiya yawan al'ummu a fadin duniya.

Ya ce ko shakka babu sakamakon da kasar Sin ta samu babban ci gaba ne da aka samu, yayin da ake kokarin tabbatar da muradun samun ci gaba mai dorewa na MDD.

Jami'in ya kara da cewa, ci gaban kasar Sin ya kasance abun koyi ga sauran kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China