Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara zuba jari a jihar Lagos dake Najeriya
2019-09-18 14:04:31        cri
Karamin jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya, Mr. Chu Maoming, ya bayyana cewa, sassa masu zaman kansu na kasar dake zuba jari, sun kammala shirye-shiryen da suka wajaba na kara yawan cinikayyar da suke yi a jihar Lagos da darajarsu ta kai biliyoyin daloli. Yana mai cewa, matakin zai taimakawa wajen samar da guraben ayyukan yi da musayar fasahohi.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana hakan ne, lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Lagos, Mr Babajide Sanwo-Olu jiya Talata.

A nasa bangare, Gwamna Sanwo-Olu ya ce, manufar shirin raya kasa na gwamnatinsa, ita ce, samarwa al'ummomin jihar ingancin rayuwa da ci gaban tattalin arziki. A cewarsa, koda yake jihar tana fama da kalubale na karuwar yawan jama'a, duk ha haka, gwamnatinsa ta shirya horas da jama'a da samar musu sana'o'i na dogaro da kai.

Gwamna Sanwo-Olu ya kara da cewa, gwamnatinsa, za ta fadada alakarta da gwamnatin kasar Sin wajen gina al'umma ta hanyar samarwa matasan jihar damammaki na samun horo a fannoni daban-daban, ciki har da fasahar keke-kere, da aikin gona, da samar da kayayyaki da gine-gine da musayar al'adu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China