Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dokokin ECOWAS ta yi kira ga Najeriya da ta canja shawara game da rufe kan iyakokinta
2019-09-18 09:23:12        cri
Majalisar dokokin kungiyar kasashen ECOWAS, ta bayyana cewa, matakin da Najeriya ta dauka na baya-bayan nan na rufe kan iyakokinta da makwabtanta dake yammacin Afirka, na iya kawo nakasu ga aiwatar ga yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Cikin wata sanarwa da majalisar kungiyar ta fitar jiya Talata a birnin Monrovia na kasar Liberiya, kungiyar ta bayyana cewa, shawarar gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokin nata, zai ci gaba da haifar da barazana wajen aiwatar da yarjejeniya game da zirga-zirgar jama'a cikin 'yanci a shiyyar.

A watan da ya gabata ne, hukumomin Najeriya suka sanar da rufe kan iyakokinsu da Benin da kuma Nijar a baya-bayan nan, a wani mataki na magance matsalar sumoga.

Majalisar ECOWAS dai ta ce, matakin na iya kawo cikas, wajen cimma babbar manufar kungiyar, da suka hada da samar da kyakkyawar makoma, budewa kasashen yankin yammacin Afirka iyakokin juna, mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China