Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kirkire-kirkire sun kara inganta karfin raya tattalin arzikin kasar Sin
2019-09-17 19:36:29        cri

Yau Talata gidan rediyon kasar Sin wato CRI, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kirkire-kirkire sun kara inganta karfin raya tattalin arzikin kasar Sin", inda aka yi nuni da cewa, bankin duniya, da cibiyar nazarin harkokin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin, da ma'aikatar kudin kasar Sin, sun gabatar da wani rahoto mai taken "Yin kirkire-kirkire a kasar Sin: Kirkire-kirkire sun kara inganta karfin raya tattalin arzikin kasar Sin" cikin hadin gwiwa.

An kuma bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin sabon tsarin ci gaba na yau da kullum, kuma yana samun ci gaba cikin sauri, yayin da karfin kirkire-kirkirensa shi ma ke kara karfafuwa yadda ya kamata.

Sabbin alkaluman hukumar kididdigar kasar Sin sun nuna cewa, alkaluman karfin inganta ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2018 ya kai 270.3, adadin da ya karu da kaso 28.7 bisa dari a kan na shekarar 2017. Dalilin da ya sa kasar Sin ta samu wannan sakamako shi ne, gwamnatin kasar Sin tana nacewa kan manufar yin kirkire-kirkire, yayin da take sa kaimi kan ci gaban kasar, wato tana amfani da karfin kasuwa, tare kuma da fitar da wasu manufofi domin nuna goyon baya ga kirkire-kirkiren da kamfanoni da kwararru suke yi.

Sharhin ya jaddada cewa, yanzu bil Adama suna cikin wani sabon zamani mai muhimmanci, na juyin juya halin fasahohi da sauye-sauyen sana'o'i, haka kuma suna fuskantar kalubaloli na bangaranci, da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, a don haka kasar Sin za ta kara shiga tattalin arzikin duniya, tare kuma da ingiza ci gaban tattalin arzikinta ta hanyar yin kirkire-kirkire, ta yadda za ta dakile rikicin da take fuskantar, tare kuma da samun ci gaba mai inganci.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China