Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasar Sin take zuba jari a ketare yana amfana wa kowa
2019-09-17 14:03:20        cri
Kwanan baya, hukumar kididdigar kasar Sin da hukumar kula da musayar kudi ta kasar sun fitar da alkaluman kididdiga dangane da yadda kasar Sin ta zuba jari a ketare kai tsaye a shekarar 2018, inda aka nuna cewa, kasar Sin ta kasance daya daga cikin kasashe uku na farko a duniya a fannin yawan jarin da kasar ta zuba a ketare kai tsaye a shekarar 2018, ta kuma zuba jari a kasashe da yankuna 188 a duniya a manyan fannoni guda 18 na tattalin arziki, lamarin da ya taimaka wa masana'antun ketare da yawansu ya wuce kaso 70 daga yin asarar kudi. Sa'an nan kuma, masana'antun ketare sun biya kudin haraji da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 59.4, kana sun dauki mazauna wurin fiye da miliyan 1.8 aiki, adadin daya wuce rabin jimillar ma'aikatan masana'antun.

Duk da rashin farfadowar tattalin arzrikin duniya, da koma bayan yin ciniki da zuba jari a duniya yadda ya kamata, da karuwar ba da kariya a harkokin ciniki, amma kasar Sin tana zuba jari a ketare ba tare da tangarda ba, lamarin da ya kara azama kan kyautata tsarin tattalin arzikinta, da inganta karfin masana'antun kirkire-kirkire da yin takara a duniya, har ma ya ba da gudummowa wajen kara samun kudin haraji da samar da guraben aikin yi a kasashen da Sin ta zuba jari. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China