Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta jinjina wa tsibirin Solomon da ta kulla huldar jakadanci da ita
2019-09-17 11:06:16        cri

Jiya Litinin 16 ga wata, gwamnatin tsibirin Solomon Islands ta tsai da kudurin yanke huldar jakadanci da yankin Taiwan, inda ya shirya kulla huldar jakadanci da kasar Sin.

Dangane da lamarin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Sin ta jinjina wa gwamnatin tsibirin da ta amince da kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, inda ta yanke hulda da Taiwan ta kuma kulla huldar jakadanci da Sin. Kasar Sin ta goyi bayan muhimmin kudurin da gwamnatin tsibirin na Solomon ya tsai da, a matsayinta na kasa mai 'yancin kai da ikon mulkin kanta.

Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin daya tak ce a duniya. Gwamnatin Sin, ita ce halaltacciyar gwamnati daya tak da ke wakiltar dukkan al'ummar Sin. Ba za a iya raba yankin Taiwan daga kasar Sin ba. Wannan shi ne hakikanin abu da kasashen duniya suka amince da shi. Kasar Sin ta kulla huldar jakadanci a tsakaninta da kasashe 178 a duniya bisa ka'idar "kasancewar kasar Sin daya tak a duniya". (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China