Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilan da ke sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki mai inganci suna karuwa a Sin
2019-09-16 19:18:09        cri

Yau Litinin gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi, wanda ya bayyana cewa, dalilan da suke sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki mai inganci a nan kasar Sin suna kara karuwa a kai a kai.

Sharhin ya yi nuni da cewa, sabbin alkaluman hukumar kididdigar kasar Sin sun nuna cewa, yanzu haka karfin bukatun gida a kasar Sin yana kara habaka, kana a cikin watanni 8 na farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar yana gudana cikin lumana, har ma ya samu ci gaba yadda ya kamata, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne matakai a jere da gwamnatin kasar Sin ta dauka. Alal misali an rage harajin da kamfanonin kasar suke bugawa, da kudin da ake biya kan inshorar zaman takewar al'ummar kasar, kuma an rage jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade. A sa'i daya kuma, an kafa yankin gwaji a birnin Shenzhen na lardin Guangdong, da sabuwar unguwar Lingang a yankin ciniki maras shinge a birnin Shanghai. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin ta kara gina yankunan ciniki maras shinge guda shida a fadin kasar.

Sharhin ya jaddada cewa, har kullum kamfanonin kasar Sin suna nacewa kan manufar yin kirkire-kirkire, domin kara kyautata tsarin tafiyar da harkokinsu, ta yadda za su taka babbar rawa yayin da ake kokarin cimma burin raya tattalin arziki mai inganci a kasar Sin.

A cikin jerin sunayen kamfanoni 500 mafiya karfi a duniya da mujallar "Fortune" ta kasar Amurka ta fitar a shekarar 2019, a karo na farko, adadin kamfanonin kasar Sin ya zarta adadin kamfanonin Amurka.

Duk da cewa tattalin arzikin duniya yana fuskatar yanayi maras tabbaci, amma tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba bisa shirin da aka tsara, kuma zai samu ci gaba sannu a hankali, lamarin da ya ci gaba da sa kaimi kan karuwar tattalin arzikin duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China