Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeria ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Disamba
2019-09-16 10:27:43        cri

 

Shugaban rikon kwarya na kasar Algeria Abdelkader Bensalah, ya sanar a jiya cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 12 ga watan Disamban bana.

Kamfanin dillancin labarai na kasar APS, ya ruwaito Abdelkader Bensalah, yayin wani jawabi da aka watsa ta kafar talabijin yana cewa, kasar ta yanke shawarar sanya ranar 12 ga watan Disamban bana a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa, yana mai cewa, lokaci ya yi da kowa zai sanya muradun kasar gaba da komai.

Ya kara da cewa, ya sanya hannu kan wata dokar shugaban kasa game da batun bisa tanadin dokoki da kundin tsarin mulkin kasar.

Abdelkader Bensalah, ya ce zaben shugaban kasar ita kadai ce mafitar siyasa, yana mai jaddada kudurinsa na yin dukkan abun da ya wajaba wajen tabbatar da gudanar sahihin zabe. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China