Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kara mayar da hankali ga batun yaki da ta'addanci a yankin kungiyar ECOWAS
2019-09-15 16:29:01        cri
An gudanar da taron koli na musamman na kungiyar ECOWAS a birnin Ouagadougo dake kasar Burkina Faso a jiya Asabar, inda shugabannin kasashe 15 membobin kungiyar da kuma na kasar Mauritania da Chadi suka halarta. Mahalartar taron sun cimma daidaito kan tattara kudi dala biliyan 1 don yaki da ta'addanci a yankin.

Shugaban kungiyar kasashe 5 na yankin Sahel wato G5 a wannan karo kuma shugaban kasar Burkina Faso mai daukar bakuncin taron kolin na musamman Christian Kabore ya bayyana cewa, a cikin wasu watannin da suka gabata, rikicin mai tsanani ya faru a yankin Sahel domin ayyukan ta'addanci da aka gudanar, wanda ya haddasa raba mutane fiye da miliyan 1 da gidajensu. Don hakan, tilas ne kasashen yammacin Afirka su yi amfani da albarkatun mutane da kayayyaki da bayanai wajen raya sojojin kiyaye tsaronsu don inganta karfin yaki da ta'addanci.

Shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karo kuma shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya bayyana cewa, sun damu da barazanar da ta'addanci ya kawo a yankin, don haka, tilas ne kasashen yammacin Afirka su yi kokari wajen kiyaye cikakken ikon mallakar yankunansu, da kuma tabbatar da tsaro da dukiyar jama'arsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China