Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira a baiwa kasashe cikakken ikon neman ci gaba
2019-09-14 16:05:31        cri

Yayin taro karo na 42 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD wato UNHRC a takaice, jakadan kasar Sin dake ofishin majalisar a Genevaļ¼Œkana wakilin Sin a sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland Chen Xu, ya gabatar da sanarwar hadin-gwiwa a madadin wasu kasashe 139, mai taken "cimma burin samun ci gaba, baiwa daukacin al'umma damar bunkasuwa".

Jakada Chen Xu ya ce, neman ci gaba babban jigo ne na zamantakewar al'umma har abada. Irin nasarorin da kasashe daban-daban suka samu, musamman kasashen dake tasowa sun shaida cewa, neman ci gaba na da matukar muhimmanci ga kare hakkin dan Adam.

Jakadan ya kara da cewa, a halin yanzu ra'ayoyin nuna bangaranci da bada kariya na ci gaba da yaduwa a duniya, matsalar da ta yiwa hadin-gwiwar kasashen duniya karan-tsaye. Ya ce har yanzu, akwai babban gibi da rashin daidaito tsakanin ci gaban kasashe daban-daban, kana ba a kawar da talauci da yunwa daga tushe, haka zalika ba a aiwatar da 'yancin ci gaba yadda ya kamata a duk fadin duniya. Jakadan na Sin, ya yi kira ga kasashe daban-daban da su mutunta sanarwar kare 'yancin ci gaba ta MDD, da tabbatar da baiwa al'ummarsu ikon samun ci gaba cikin adalci, ta yadda kowa da kowa zai yi rayuwa cikin mutunci.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China