Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani jirgi mai dauke da mahajjata ya yi saukar karfi a Nijeriya
2019-09-08 15:40:53        cri
Jirgin sama kirar Boeing 747, dauke da fasinjoji sama da 550, ya yi wata saukar karfi jiya Asabar a garin Minna, babban birnin jihar Niger dake arewa maso tsakiyar Nijeriya, bayan ya samu matsala a kokarinsa na sauka.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Jirgin mai dauke da mahajjatan da suka koma gida daga aikin hajjin bana, ya gamu da matsala ne a lokacin da yake kokarin sauka, lamarin da ya tilasta masa sauka da karfi, sai dai babu wanda ya mutu a sanadin lamarin.

Jirgin mallakin kamfanin jeragen sama na Max Air ne, wanda kawo yanzu bai tabbatar da aukuwar lamarin ba.

Sai dai kakakin hukumar kula da jin dadin alhazai na jihar, Hajiya Hassana Isa, ta shaidawa manema labarai cewa, lamarin ba zai hana aikin jigilar alhazai sama da 2,000 dake Saudiyya zuwa gida ba.

Wata majiyar tsaro daga filin jirgin saman birnin, ta shaidawa Xinhua cewa, titin jirgi da sauran wasu kayayyaki na filin jirgin saman sun lalace sanadiyyar saukar karfi da jirgin ya yi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China