Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar manzon musammam na Shugaba kasar Sin a Nijeriya ta cimma manufarta
2019-09-06 14:19:37        cri

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya bayyana ziyarar, Yang Jiechi, manzon musammam na shugaban kasar Sin Xi Jinping a Nijeriya, a matsayin wadda ke da ma'ana ga kasar dake yammacin Afrika.

Geofrrrey Onyeama ya ce ziyarar ta yi ma'ana. Kuma suna farin ciki da kudurin kasar Sin na karfafa dangantaka da Nijeriya ta kowacce fuska.

Ministan ya kuma bayyana cewa, ziyarar ta nuna kudurin kasar Sin na inganta dangantakarta da Nijeriya da kuma aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika (FOCAC) da aka yi a shekarar 2018. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China